16 Nuwamba 2020 - 13:35
​Macron Ya Bukaci Turai Ta Samarda Tsarin Tsaro Na Kanta Wanda Amurka Bata Ciki

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewa, ko da sabuwar gwamnatin Amurka mai shigowa ta dawo ta hada kai da kasashen yankin a harkokin tsarin nahiyar, akwai bukatar kasashen nahiyar ta Turai su mallaki tsarin tsaron kasashensu wanda Amurka bata ciki.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto Macron ya fadar haka a jiya Lahadi a lokacinda yake maida martani ga ministan tsaron kasar Jamus.

Macron ya kara da cewa, ya na tsammanin waziriyar kasar ta Jamus Angela Merkel ma tana da tunani irin nasa, kuma idan kasashen turai sun yi hakan, to Amurka za ta kasance mai kasa wacce aikin tare da kasashen na Turai ba wacce ta ke da wuka da nama kan harkokin tsaron kasashen yankin ba.

342/